Zaben Gwamna: APC tayi martani a kan nasarar da Adeleke ya yi a kotu

Zaben Gwamna: APC tayi martani a kan nasarar da Adeleke ya yi a kotu

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Osun ta mayar da martani a kan kwace nasarar lashe zaben gwamna daga hannun dan takararta Gboyega Oyetola inda aka mika wa Ademola Adeleke na PDP.

Jam'iyyar ta ce nasarar da kotun sauraron karraakin zabe ta bawa Ademola Adeleke na PDP a matsayin gwamna ba nasara ba ce da za ta dore.

Kotun wadda ta bar Osogbo zuwa Abuja domin sauraron karar saboda kallubalen tsaro ta ce Ademola na ainihin wanda ya lashe zaben.

Kotun ta ce dan takarar PDP ne ya lashe zaben na farko inda ta ce zaben karo na biyo ba bisa ka'ida aka yi shi ba.

DUBA WANNAN: Abin azimun ne: An kara tura kwamishinonin zabe uku jihar Kano

Zaben gwaman Osun: APC tayi tsokaci a kan nasarar Adeleke
Zaben gwaman Osun: APC tayi tsokaci a kan nasarar Adeleke
Asali: Twitter

Sakamakon zaben na farko da aka yi a ranar 19 ga watan Satumba ya nuna PDP ce tayi nasara da kuri'u 254,698 yayin da APC ta samu 254,345votes.

An sake zaben karo na biyu a ranar 27 ga watan Satumba inda jam'iyyar APC ta samu kuri'u fiye da PDP.

A yayin da ya ke mayar da martani, sakataren watsa labarai na APC a jihar Osun, Kunle Oyatomi ya ce hukuncin da kotun da zartar ba zai dore ba idan aka tafi babban kotu.

"Za mu daukaka kara kuma da izinin Allah mun san wannan hukuncin ba zai dore ba," inji shi.

"Hukuncin kotun ya janyo mana koma baya kadan amma mun san cewa kotun daukaka kara ko kotun koli za tayi fatali da hukuncin.

"Babu bukatar al'umma su tayar da hankulansu, muna kira ga magoya bayan mu su kwantar da hankulansu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel