Hukuncin kotu kan zaben gwamnan Osun: Atiku ya taya Adeleke murna

Hukuncin kotu kan zaben gwamnan Osun: Atiku ya taya Adeleke murna

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabreru, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya Sanata Ademola Adeleke murnar samun nasarar karar da ya shigar a kotu.

Da ya ke taya Adeleke murnar samun nasara a kotun, Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 22 ga watan Maris cewa fannin shari'a ne kadai madafar talaka da ta rage a kasar kuma fannin da zai kare demokaradiyya a kasar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa; kotun da ke sauraron korafe korafen zaben gwamnan jihar Osun da ke da zama a babban birnnin tarayya Abuja ta bayyana jam'iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2018, Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

KARANTA WANNAN: Yanzu: Kotu ta tabbatar da Adeleke na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Osun

Hukuncin kotu kan zaben gwamnan Osun: Atiku ya taya Adeleke murna
Hukuncin kotu kan zaben gwamnan Osun: Atiku ya taya Adeleke murna
Asali: Twitter

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa ba jam'iyyar APC da dan takararta, Gboyega Oyetola ba ne suka lashe zaben, don haka ta kwace nasarar da aka baiwa jam'iyyar bayan zaben jihar zagaye na biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel