Yanzu: Kotu ta tabbatar da Adeleke na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Osun

Yanzu: Kotu ta tabbatar da Adeleke na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Osun

Kotun da ke sauraron korafe korafen zaben gwamnan jihar Osun da ke da zama a babban birnnin tarayya Abuja ta bayyana jam'iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2018, Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa ba jam'iyyar APC da dan takararta, Gboyega Oyetola ba ne suka lashe zaben, don haka ta kwace nasarar da aka baiwa jam'iyyar bayan zaben jihar zagaye na biyu.

Dan takarar jamiyar APC, Gboyega Oyetola ya doke abokin takarar sa na jamiyar adawa ta PDP, Ademola Adeleke, a zaben gwamnan jihar Osun da aka sake gudanarwa zagaye na biyu da tazarar kuri'u 483.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Nigeria ta mayar da wasu 'yan Ghana guda 4 kasarsu akan karya doka

Sanata Adeleke tare da mawaki Davido
Sanata Adeleke tare da mawaki Davido
Asali: Instagram

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da sakamakon zaben bayan karashen zaben da aka gudanar a wasu mazabu da aka dakatar da zaben su.

Sai dai bayan sanar da sakamakon zaben, Sanata Adeleke da jam'iyyarsa ta PDP sun garzaya kotun sauraron korafe korafen zaben gwamnan, inda suka bayyana cewa ba su amince da sakamakon zaben ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel