Zaben 2019: Amurka tace an yi cinikin kuri’u sosai da kuma razana masu zabe

Zaben 2019: Amurka tace an yi cinikin kuri’u sosai da kuma razana masu zabe

Gwamnatin kasar Amurka ta nuna rashin jin dadi kan yadda zaben 2019 ya gurbace da abubuwan da suka saba ka’ida.

Gwamnatin ta Amurka ta ce daga rahotannin da ta samu daga masu sanya-ido a zabe, an samu yawaitar tsorata masu zabe, an ci kasuwar cinikin kuri’u, jami’an tsaro sun yi wa harkar zabe shiga-sharo-ba-shanu, sannan kuma a wurare da dama an samu hargitsi da tashe-tashen hankula wanda rikita tsarin gudanarwar zaben a sassa da yawa cikin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wani rubutaccen sakon jawabi da Kasar Amurka ta saki a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Zaben 2019: Amurka tace an yi cinikin kuri’u sosai da kuma razana masu zabe
Zaben 2019: Amurka tace an yi cinikin kuri’u sosai da kuma razana masu zabe
Asali: UGC

Amuka ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a cikin zabe da kuma jami’an tsaro da su tabbatar da an gudanar da zabe cikin lumana, a yi adalci, kada a yi magudi ko murdiyya a zabukan da za a yi ranar Asabar a yankunan da INEC ta ce zabe bai kammalu ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kafa kwamitin bada cin gashin kai ga majalisun jihohi da fannin shari'a

Daga nan kuma Amurka ta mika sakon ta’aziyyar ta ga iyalan wadanda rikicin zaben 2019 ya yi sanadin rasa rayukan su.

kasar ta sake jaddada cewa ita fa ba ta da wani dan takara da take goya wa baya, amma dai za ta ci gaba da bayar da goyon bayan da ta ke yi wajen ganin ingantacciyar dimokradiyya ta ginu, kuma ta tsaya da kafafun ta a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel