Sule Lamido ya fadi yadda APC da Kwamishinan 'yan sanda suka yiwa PDP magudin zabe

Sule Lamido ya fadi yadda APC da Kwamishinan 'yan sanda suka yiwa PDP magudin zabe

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya ce Kwamishinan 'yan sandan jihar Jigawa, Bala Senchi ya hada kai da jam'iyyar All Progressives Party (APC) sunyi magudin zabe a zabukan da akayi a Jihar.

Ya ce shugaban 'yan sandan ya kama 'yan jam'iyyar PDP sama da 100 a jihar ciki har da hadiminsa a kan sabuwar kafar watsa labarai, Mansur Ahmed a lokacin zabukan shugaban kasa, gwamna da 'yan majalisun jiha.

"'Yan sanda sun yiwa hadimi na sharri. Sun saka takardun kada kuri'a na INEC a jikinsa a ranar zabe. Sun saka masa ankwa kuma aka tafi dashi gidan yari kuma duk hotunansa sun karade shafukan sada zumunta," inji Lamido.

Kwamishinan 'yan sanda Senchi ya taya APC yin magudi a Jigawa - Sule Lamido
Kwamishinan 'yan sanda Senchi ya taya APC yin magudi a Jigawa - Sule Lamido
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

"Kwamishinan 'yan sandan ya yi amfani da karfin ikonsa ya musgunawa masu kada kuri'a kawai domin sun nuna son PDP. Ina fatan ya yi tsawon rai domin ya girbe muguntan da ya yi mana. Ina fata shi da iyalansa ba za su taba samun natsuwa ba saboda zaluncin da ya yiwa al'ummar Jigawa"

Lamido ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Dutse babban birnin Jihar Jigawa jim kadan bayan ya kira taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a jihar inda suka yi nazarin sakamakon zaben.

Ya ce an yiwa kwamishinan zaben canjin wurin aiki amma Gwamna Muhammadu Badaru ya garzaya Abuja ya dakatar da hakan saboda yana bukatan ya tsaya a jihar ya taya APC magudin zabe. "Ya aikata dukkan abinda aka umurce shi," inji Lamido.

Ya bayar da misalin da abinda ya faru a garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji inda Kwamishinan 'yan sanda ya sa aka tsare wani dattijo da matarsa da yaransu biyu da ke karatu a jami'ar ABU Zaria saboda sunyi yunkurin kare hakkin PDP a unguwarsu.

A bangarensa, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mr Senchi ya musanta dukkan zargin da Sule Lamido ya yi a kansa. Ya ce Sufeta Janar na 'yan sanda ne ke da ikon canja masa wurin aiki saboda haka ba zai ce komi a kan hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel