Buhari ya kafa kwamitin bada cin gashin kai ga majalisun jihohi da fannin shari'a

Buhari ya kafa kwamitin bada cin gashin kai ga majalisun jihohi da fannin shari'a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin Shugaban kasa akan cin gashin kan majalisun jiha da bangaren shari’a na jiha kamar yadda yake kundin tsarin mulki.

Kwamitin mai dauke da mutane 16 ya hada da ministan shari’a kuma babban atoni janar na kasa, Abubakar Malami a matsayin shugaba, yayinda mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Ita Enang zai kasance sakataren kwamitin.

Yayin da yake kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Buhari ya bukaci mambobin kwamitin da su sanya kwazo wajen gudanar da aiki.

Buhari ya kafa kwamitin bada cin gashin kai ga majalisun jihohi da fannin shari'a
Buhari ya kafa kwamitin bada cin gashin kai ga majalisun jihohi da fannin shari'a
Asali: Depositphotos

Shugaban kasar, wanda yace kwamitin na da nan da watanni uku don kammala aiki, ya bukaci mambobin kwamitin da su tabbatar da yin aiki bisa tsari.

Buhari yace: “Ina farin cikin yi maku barka da zuwa wajen bikin kaddamar da kwamitin Shugaban kasa kan ba bangarorin majalisun jiha da na shari’an jiha cin gashin kansu. An kafa kwamitin duba ga cewr akwai bukatar ma majalisar dokoki da bangaren shari’a ikon cin gashin kansu kamar dayya damokradiyarmu ta tanadar.

KU KARANTA KUMA: Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno

“Mun jajirce wajen karfafa damokradiyarmu ta hanyar raba mulki tsakanin bangarorin gwamnati guda uku, har a matakan jiha. Muna ganin akwai bukatar raya kundin tsarin mulkin gwamnati ta hanyar gina karfafan iko ba wai a matakin tarayya kadai ba, harma ga dukkanin jihohin kasar.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel