Boko Haram: Rundunar soji ta gina ma'aikatar burodi domin ciyar da dakarunta

Boko Haram: Rundunar soji ta gina ma'aikatar burodi domin ciyar da dakarunta

- Rundunar soji ta gina ma'aikatar burodi domin ciyar da dakarunta na bataliyar hadin guiwa ta 115, da ke atisayen LAFIYA DOLE a garin Askira-Uba, jihar Borno

- Rundunar sojin ta ce an gudanar da gina kamfanonin guda biyu karkashin kwamandan bataliyar ayyukan jin kai na rundunar

- A cewar rundunar sojin, babbar makasudin gina kamfanonin guda biyu shine samar da abinci mai lafiya da gina jiki ga sojojin

Dakarun sojin bataliyar hadin guiwa ta 115, da ke atisayen LAFIYA DOLE a garin Askira-Uba, sun gina wani kamfanin sarrafa burodi (mummuki) da kuma ruwan leda domin ciyar da sojojin da ke yaki da mayakan Boko Haram a Borno.

Manjo Yusuf Salisu, kwamandan hadin guiwar bataliyar ta 115, ya bayyana hakan a wata ziyarar aiki da Birgediya Janar Bulama Biyu; mukaddashin babban kwamandan rundunar soji ta 7 ya kai masa a ranar Juma'a.

Salisu, wanda ya samu wakilcin Manjo Godwin Ameh, ya ce an gudanar da gina kamfanonin guda biyu karkashin kwamandan bataliyar ayyukan jin kai na rundunar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Nigeria ta mayar da wasu 'yan Ghana guda 4 kasarsu akan karya doka

Boko Haram: Rundunar soji ta gina ma'aikatar burodi domin ciyar da dakarunta
Boko Haram: Rundunar soji ta gina ma'aikatar burodi domin ciyar da dakarunta
Asali: UGC

Ya ce wannan ci gaban ya na daga cikin yunkurin rundunar sojin na kare dakarunta daga sha ko cin abinci da bai dace da lafiyarsu ba ko kuma abincin da ke da guba daga Boko Haram ko masu goyon bayansu.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin burodin da ake sayarwa a kasuwa na dauke da sinadaran sanya cutar kansa a jikin dan Adam, da suka hada da Potassium Bromate da Potassium Iodate, wadanda kuma sinadarai ne da aka haramta amfani da su a Nigeria.

A cewarsa, babbar makasudin gina kamfanonin guda biyu shine samar da abinci mai lafiya da gina jiki ga sojojin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel