Sake zabe: INEC ta soma rabon kayayyakin zabe a Benue

Sake zabe: INEC ta soma rabon kayayyakin zabe a Benue

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace ta yi rabon kayayyakin aiki a fadin kananan hukumomi 23 dake Benue duk a cikin shirin sake zaben gwamna a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Mista Terkaa Andyarigeria, kakakin hukumar INEC na jihar, ya bayyana hakan a hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta wayar talho a Makurdi.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta tattaro cewa za a gudanar da sake zaben gwamnoni a kananan hukumomi 22 daga cikin hukumomi 23 dake jihar.

Sake zabe: INEC ta soma rabon kayayyakin zabe a Benue
Sake zabe: INEC ta soma rabon kayayyakin zabe a Benue
Asali: Instagram

NAN ta rahoto cewa karamar hukumar da baza a sake gudanar da zaben gwamna ba guda ce wato karamar hukumar Katsina-Ala.

KU KARANTA KUMA: Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno

Duk da haka, za a sake gudanar da zaben majalisan jiha a Katsina-Ala da wassu kananan hukumomi guda tara a jihar.

Za a gudanar da zaben a wuraren da ba a gudanar da zabe ba a baya da kuma wutaren da aka soke zabe, wannan yana nunin cewa ba gaba daya karamar hukumar za a gudanar da zaben ba.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sharadi guda daya wacce a karkashinta ne za ta bai wa gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha takardan shaidan cin zabe.

A wani taro na manema labarai a Abuja, Festus Keyamo, shugaban kwamitin labarai da ilimantar da masu zabe, yace hukumar za ta bai wa Okorocha takardan shaidan cin zabe ne idan kotu ta bada umurnin yin haka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel