Yadda Okorocha zai iya samun takardar shaidar cin zabe – INEC

Yadda Okorocha zai iya samun takardar shaidar cin zabe – INEC

- Hukumar zabe ta bayyana sharadi guda daya wacce a karkashinta ne za ta bai wa gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha takardan shaidan cin zabe

- INEC tace bisa umurnin kotu ne kadai za ta iya bai wa Okorocha takardar cin zabe

- Gwamna Rochas Okorocha dai ya shigar da kara kotu ne bayan hukumar zabe ta hana masa takardar shaidar cin zaben Sanata da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sharadi guda daya wacce a karkashinta ne za ta bai wa gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha takardan shaidan cin zabe.

A wani taro na manema labarai a Abuja, Festus Okoye, shugaban kwamitin labarai da ilimantar da masu zabe, yace hukumar za ta bai wa Okorocha takardan shaidan cin zabe ne idan kotu ta bada umurnin yin haka.

Bisa umurnin kotu ne kadai za mu ba Okorocha takardar shaidar cin zabe - INEC
Bisa umurnin kotu ne kadai za mu ba Okorocha takardar shaidar cin zabe - INEC
Asali: Twitter

Fransis Ibeawuchi, jami’in zabe na yankin Imo maso yamma a zaben majalisan dattijai, ya bayyana Okorocha a matsayin wanda ya lashe zabe.

Amman hukumar INEC ta ki bai wa Okorocha takardan shaida saboda Ibeawuchi ya bayyana cewa tursasa shi aka yi ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

KU KARANTA KUMA: Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno

Wannan yasa Okorocha kai karar hukumar kotu. A wata kara da aka shirya a babban kotun tarayya da ke Abuja, gwamnan ya bukaci kotun da ta yanke hukuncin cewa hukumar INEC bata da karfin hana shi takardan shaidarsa sannan ta bada umurnin cewa hukumar ta mika mishi takardan shaidarsa.

A lokacin da aka bukaci ya bayyana ra’ayinsa akan lamarin, Okoye yace matsayin hukumar ba zata amince da rashin bin ka’idojinta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel