Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno

Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno

- Rahotanni sun nuna cewa yan gudun hijira a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno sun gudanar da zanga-zanga

- Sun yi zanga-zangan ne akan zargin karancin abuinci a sansanin nasu

- Mafi akasarin masu zanga-zangar sabbin zuwa ne daga Kukawa da Kalabalge, kananan hukumomin da yan ta’adda suka fatattaka a farkon wannan shekarar

Yan gudun hijira a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno sun yi zanga-zanga akan karancin abinci a sansaninsu.

Maza, mata da yara da ke saune a sansanin yan gudun hijira na hanyar Gubio a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris sun tunkari masu aikin agaji kan abunda suka bayyana a matsayin matsananciyar hali.

Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno
Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga kan karancin abinci a Borno
Asali: UGC

Mafi akasarin masu zanga-zangar sabbin zuwa ne daga Kukawa da Kalabalge, kananan hukumomin da yan ta’adda suka fatattaka a farkon wannan shekarar, wanda suka ce ana tursasasu kwana a waje a filin Allah.

Sai da jami’an tsarn sansanin suka shiga lamarin sannan suka tura masu zanga-zangar baya yayinda suka yi barazanar shiga unguwanni.

KU KARANTA KUMA: Musulmai daga yankin Yarbawa sun bukaci Buhari ya basu kujerun ministoci

Sansanin Gubo na dauke da sama da mutane 28,000 wadanda mafi akasarinsu daga Munguno, kukawa da Kalabalge naa jihar Borno.

A wani lamari na daban, mun ji cewa rundunar sojin Najeriya a ranar Juma’a, 22 ga watan Maris ta yalwata atisayen ta na nuna karfi zuwa kananan hukumomi shida da ke fama da yamutsi a jihar Sokoto yayinda ake shirya ma zaben da za a sake a ranar Asabar a jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da Raba, Kebbe, Gada, Goronyo, Sabon Birni da kuma Isa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel