Da duminsa: Nigeria ta mayar da wasu 'yan Ghana guda 4 kasarsu akan karya doka

Da duminsa: Nigeria ta mayar da wasu 'yan Ghana guda 4 kasarsu akan karya doka

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta iza keyar wasu 'yan kasar Ghana guda hudu zuwa kasarsu akan abunda ta kira karya dokokin shige da fice na kasar

- Umurnin wacce aka bayar da ita akan kare 'yancin al'umma, ya shafi mata 3 da mace daya. Sun hada da Florence Donkur, Simon Gyan, Yeboah Collins da Alhaji Isa.

- Kwanturolan NIS Muhammad Babandede, ya tabbatar da yunkurin hukumar na tabbatar da cewa masu shigowa kasar sun bi dokokin da kasar ta tanadar sau da kafa

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta iza keyar wasu 'yan kasar Ghana guda hudu zuwa kasarsu akan abunda ta kira karya dokokin shige da fice na kasar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar kula da shige da fice ta kasa NIS ya rabawa manema labarai a ranar Juma'a a Abuja.

Sanarwar ta ce: "Hukumar shige da fice ta iza keyar wasu 'yan kasar Ghana guda hudu zuwa kasar su, bisa umurnin ministan cikin gida, bayan da aka same su da karya dokokin shige da fice ta kasar Nigeria.

KARANTA WANNAN: Shugabancin majalisar tarayya ta 9: Zababbun sanatocin APC sun gargadi jam'iyyar

Da duminsa: Nigeria ta mayar da wasu 'yan Ghana guda 4 kasarsu akan karya doka
Da duminsa: Nigeria ta mayar da wasu 'yan Ghana guda 4 kasarsu akan karya doka
Asali: Depositphotos

"Wannan kuwa na ya faru ne sakamakon karfin ikon da aka ratayawa ministan cikin gida a sashe na 45 sakin layi na 1 zuwa na 2 na dokar shige da fice ta kasa da aka samar a shekara ta 2015.

"Umurnin wacce aka bayar da ita akan kare 'yancin al'umma, ya shafi mata 3 da mace daya. Sun hada da Florence Donkur, Simon Gyan, Yeboah Collins da Alhaji Isa.

"An iza keyarsu zuwa kasarsu ta asali ta hanyar babban jirgin sauka da tashi na jiragen sama na Nnamdi Azikwe, Abuja a ranar Juma'a 22 ga watan Maris, 2019 da misalin karfe 9 na safiya.

"Kwanturolan hukumar shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede, ya yi amfani da wannan damar wajen tabbatar da yunkurin hukumar na kakaba dokoki a duk lokakacin da bukatar hakan ta taso domin tabbatar da cewa masu shigowa kasar sun bi dokokin da kasar ta tanadar sau da kafa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel