Maimaita zabe: Sojoji sun yi atisayen nuna karfi a kananan hukumomi 6 na Sokoto

Maimaita zabe: Sojoji sun yi atisayen nuna karfi a kananan hukumomi 6 na Sokoto

Rundunar sojin Najeriya a ranar Juma’a, 22 ga watan Maris ta yalwata atisayen ta na nuna karfi zuwa kananan hukumomi shida da ke fama da yamutsi a jihar Sokoto yayinda ake shirya ma zaben da za a sake a ranar Asabar a jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da Raba, Kebbe, Gada, Goronyo, Sabon Birni da kuma Isa.

Da yake jawabi kafin barin Sokoti, Manjo Janar Hakeem Otiki, babban kwamandan sojoji na sashi 8, yace shirin ya kasance na jan hankalin jama’a don su san da kasancewar sojoji.

Maimaita zabe: Sojoji sun yi atisayen nuna karfe a kananan hukumomi 6 na Sokoto
Maimaita zabe: Sojoji sun yi atisayen nuna karfe a kananan hukumomi 6 na Sokoto
Asali: Depositphotos

Otiki yayi bayanin cewa ba wai za a gudanar da shirin don tsoratar da jama’a bane, sai don nuna masu shirin sojoji na dakile duk wani rikici da zai damu jama’a.

Ya ci gaba da cewa shirin zai kuma kasance gargadi ga yan iska ko wasu da ke shirin tarwatsa zaben da za a sake.

Kwamandan ya kara da cewa an gudanar da wani shiri makamancin haka na tsawon waso sa’o’i a garin Sokoto a ranar Alhamis sannan ya bukaci mutane das u ba hukumomin doka hadin kai domin tabbatar da warzuwan zaman lafiya a kasar.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kano: INEC ta shirya ma zabe a kananan hukumomi 28

Sannan kumaya gargadi duk wasu masu tada zaune tsaye da su hankalta, inda ya kara da cewa a koda yaushe a shirye sojoji suke domin kare rayuka da martabar kasar.

An tattaro cewa atisayen shirin hadin gwiwa ne tsakanin rundunar sojin sama, yan sandan Najeriya, sashin yan sandan DSS, da kuma rundunar NSCDC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel