Musulmai daga yankin Yarbawa sun bukaci Buhari ya basu kujerun ministoci

Musulmai daga yankin Yarbawa sun bukaci Buhari ya basu kujerun ministoci

Yayin da daukacin 'yan Najeriya ke cigaba da dakun mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari zai nada matsayin ministoci a zabgon wa'adin mulkin sa na biyu, wata kungiya ta musulmai dake rajin kare hakkin musulmai musamman ma a yankin kasar Yarbawa ta bukaci ya ba su wasu kujeru.

Kungiyar ta Muslim Rights Concern (MURIC) a takaice ta bayyana wannan matsayar ta ta ne a cikin wata takardar da suka aike ga shugaban kasar dauke da sannun shugaban ta ranar Juma'ar, Farfesa Ishaq Akintola.

Musulmai daga yankin Yarbawa sun bukaci Buhari ya basu kujerun ministoci
Musulmai daga yankin Yarbawa sun bukaci Buhari ya basu kujerun ministoci
Asali: UGC

KU KARANTA: An tuhumi ministan Buhari kan tafka laifi

Haka nan kungiyar ta bayyana takaicin ta akan abin da ta kira irin cin kashin da ake yiwa musulmai a yankin na kudu maso yammacin Najeriya inda a lokuta da dama sukan tashi a tutar babu wajen rabon ministoci duk kuwa da yawan su.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayar da karin haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu inda yace zai gudanar da gwamnatin sa ne a faifai kuma wadda zata tabbatar da adalci ga kowa.

Haka ma dai shugaban kasar wanda ya doke dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar da ya gabata, ya ce wa'adin mulkin sa zai mayar da hankali sosai a fannin tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel