Babu kasar da ba a samun korafe-korafe bayan zabe a duk duniya: Martanin INEC ga Amurka

Babu kasar da ba a samun korafe-korafe bayan zabe a duk duniya: Martanin INEC ga Amurka

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta mayar da martani a kan sanarwar da kasar Amurka ta fitar game da babban zaben 2019 da aka gudanar a Najeriya.

Amurka ta ce bata ji dadin yadda yawancin al'umma ba su fito zaben ba tare da amfani fiye da sojoji fiye da kima a yayin gudanar da zabukan.

Wani sashi na cikin sakon da Amurka ta fitar ya ce: "A matsayin mu na tsaffin abokan huldar Najeriya, za mu cigaba sanya idanu a kan zaben da ake gudanarwa. Ba mu da wata jam'iyyar ko dan takara da muke goyon baya.

"Kamar yadda yawancin masu sanya idanu a zaben suka ruwaito, bamu ji dadin yadda al'umma basu fito sosai ba domin kada kuri'u da sayan kuri'u da rikici da kuma amfani da sojoji wurin cin zarafin mutane a wasu wurare.

DUBA WANNAN: 'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

Babu inda aka taba yin zabe ba tare da cikas ba: Martanin INEC ga Amurka
Babu inda aka taba yin zabe ba tare da cikas ba: Martanin INEC ga Amurka
Asali: Instagram

"Munyi bakin ciki a kan rikicin da wasu suka tayar kuma muna mika ta'aziyar mu ga iyalan wadanda abin ya shafa har da ma'aikatan INEC da jami'an tsaro.

"A yanzu da zaben ke zuwa karshe muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar an gudanar da sahihitar zabe kuma cikin zaman lafiya musamman a wuraren da za a yi zabe a ranar Asabar."

Sai dai a bangarensa, babban sakataren watsa labarai na INEC, Rotimi Oyekanmi ya ce an samu gagarumin nasara a zaben.

Ya ce ba za a ce ba a samu korafe-korafe ba a zaben ba amma babu wata kasa a duniya inda ake gudanar da babban zaben kasa tun farko zuwa karshe ba tare da an samun korafi ba ba ko cin karo da cikas.

Ya cigaba da cewa: "Hukumar INEC tana mika godiyarta ga Amurka a kan goyon baya da kulawa da Najeriya musamman lokacin gudanar za zaben.

"Sai dai, babu wata kasa a duniya da ake gudanar da babban zabe tun daga farko zuwa karshe ba tare da samun matsaloli ba. Idan akayi la'akari rahotannin da masu sanya idanu na gida da kasashen waje suka fitar, zamu iya cewa an samu nasara a zaben 2019 duk da cewa an samu kura-kurai."

Ya ce, a bangarenta INEC za ta cigaba da kokari domin shirya tsafatatacen zabe da al'umma za suyi na'am da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel