Mun gargadi Okorocha amma ya yi kunnen kashi - APC

Mun gargadi Okorocha amma ya yi kunnen kashi - APC

Shugaban hadin gwiwa na 'ya'yan jam'iyyar APC reshen jihar Imo, Dacta Theodore Ekechi ya jinjinawa mambobin kungiyarsu da al'ummar jihar Imo a kan rashin amincewa da su kayi Gwamna Rochas Okorocha ya kakaba musu surukinsa, Uche Nwosu a matsayin magajinsa.

Hadakar ta kunshi hadiman gwamna Rochas da ke aiki tare da shi da kuma tsaffin hadimansa da suka ajiye aiki ko aka sallame su.

A hirar da Ekechi ya yi da wakilin Daily Trust a Owerri, ya ce ba don jajircewa da juriya irin na al'ummar jihar Imo ba, da yanzu "Sarki mai cikaken iko mu ke da shi a Imo".

DUBA WANNAN: Kano: Na hannun daman Atiku ya kare shi a kan goyon bayan Abba Gida-Gida

Mun gargadi Okorocha amma ya yi kunnen kashi - APC
Mun gargadi Okorocha amma ya yi kunnen kashi - APC
Asali: Twitter

Kungiyar ta yi zargin cewa gwamnan ya bari matarsa ta tilasta wa al'umma jihar Imo surukinsu a matayin gwamna. Baya ga haka, shugabancin mara kan gado da cin amana da rashin mayar da hankali a kan muhimman al'amura da ya janyo APC ta rasa kujerun gwamna da na majalisun tarayya a jihar.

Ekechi ya ce girman kai da giyan mulki ne ya hana Okorocha sauraron shawarwari masu amfani a lokacin da ya kwallafa ransa a kan cewa dole sai surukinsa ya gaje shi.

A yayin da ya nuna rashin jin dadinsa a akan rashin nasarar da jam'iyyar APC tayi a zabukan shugaban kasa, gwamna da 'yan majalisun jiha da tarayya, Ekechi ya ce ba suyi mamakin sakamakon zaben ba domin sun gargadi gwamnan cewa tilastawa al'umma wanda ba su so ba zai haifar wa jam'iyyar da mai ido ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel