Saraki ya fi kowa yin asara a zaben 2019 – Kungiyar BMO

Saraki ya fi kowa yin asara a zaben 2019 – Kungiyar BMO

- Kungiyar BMO ta bayyana cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne yayi babban asara a zaben 2019

- BMO ta bayyana Saraki a matsayin wani dan siyasa mai ji da kansa da yayi saurin rasa ikonsa sannan ya rasa tudun dafa wa

- Tace Saraki ya mayar da kansa mara fada aji ta fannin siyasa kamar yadda al’umman mazabarsa suka waye sannan suka ba jam’iyyar All Progressives Congress (APC) goyon bayansu

Kungiyar labaran Shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Buhari Media Organisation (BMO) ta bayyana cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ne yayi babban asara a zaben 2019, saboda ya rasa abubuwa da dama a mulki sannan kuma cewa siyasarsa gab take da zama tarihi.

Kungiyar magoya bayan Shugaban kasar ta bayyana Saraki a matsayin wani dan siyasa mai ji da kansa da yayi saurin rasa ikonsa sannan ya rasa tudun dafa wa.

Saraki ya fi kowa yin asara a zaben 2019 – Kungiyar BMO
Saraki ya fi kowa yin asara a zaben 2019 – Kungiyar BMO
Asali: Depositphotos

A wani jawabi dauke da sa hannun Shugaban kungiyar, Niyi Akinsiju da babban sakatarenta, Cassidy Madueke, kungiyar tace furucin Saraki na cewa nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa ba mai yiwuwa bane ya zamo hargagin wani dan siyasa mara tasiri.

KU KARANTA KUMA: Jihar Niger za ta kashe N3.2bn wajen gyara gidan gwamnati

Kungiyar ta kuma bayyana cewa a karshe dai Saraki ya mayar da kansa mara fada aji ta fannin siyasa kamar yadda al’umman mazabarsa suka waye sannan suka ba jam’iyyar All Progressives Congress (APC) goyon bayansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel