Abin azimun ne: An kara tura kwamishinonin zabe uku jihar Kano

Abin azimun ne: An kara tura kwamishinonin zabe uku jihar Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta aike da karin kwamishinonin zabe uku zuwa jihar Kano domin sanya idanu a kan zaben raba gardama da za a gudanar a jihar a ranar Asabar 23 ga watan Maris.

Kwamishinonin zaben da aka aike zuwa Kano sun hada da Farfesa Asama'u Sani Maikudi na jihar Zamfara, Farfesa Ganiyu Raji na jihar Ogun da Alhaji Ahmad Mahmud na jihar Kebbi.

A yayin bayar da sanarwar, Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Risqua Arabi Shehu ya ce INEC a shirye ta ke ta gudanar da sahihiyar zabe a jihar.

DUBA WANNAN: CP Mohammed Wakili 'Singham' ya nemi afuwar kungiyar NBA reshen Kano

Sunaye: An karo kwamishinonin zabe uku domin zaben Kano
Sunaye: An karo kwamishinonin zabe uku domin zaben Kano
Asali: UGC

Za a gudanar da zaben raba gardamar ne a kananan hukumomi 28 na jihar. An kada kuri'u fiye da adadin mutanen da aka tantance a wasu kananan hukumomin, an kuma soke zabuka a kananan hukumomi 15 saboda rikici da ya barke.

Risqua ya ce hukumar za ta mayar da hankali domin ganin an kammala zaben a ranar Asabar.

Ya ce: "Muna aiki tukuru domin ganin ba a samu cikas ba a zaben.

"Munyi taro da dukkan jam'iyyun siyasa kuma mun sanar da su cewa kofar mu a bude ta ke a ko yaushe domin muyi duk wani abu da bai saba wa doka ba domin yiwa kowa adalci".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel