Wani babban Lauya a Najeriya ya tuhumi ministan, Malami Buhari da karya doka

Wani babban Lauya a Najeriya ya tuhumi ministan, Malami Buhari da karya doka

Wani babban Lauya a Najeriya kuma mai rajin kare hakkin dan adam, Mista Femi Falana ya rubutawa ministan shari'a kuma babban Antoni Janar na tarayyar Najeriya a gwamnatin Shugaba Buhari yana tuhumar sa da aikata ba daidai ba da aka maida wasu 'yan Kamaru kasar su.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata wasikar da ya aike zuwa ga ministan a matsayin sa na wanda ke kula da harkokin shari'a da kuma ya rabawa manema labarai ciki hadda majiyar mu ta ThisDay.

Wani babban Lauya a Najeriya ya tuhumi ministan, Malami Buhari da karya doka
Wani babban Lauya a Najeriya ya tuhumi ministan, Malami Buhari da karya doka
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari yayi karin haske akan irin gwamnatin da zai yi a wa'adi na biyu

A cewar lauyan, 'yan gudan hijira masu neman mafaka ne kuma dokoki da dama ciki hadda kundin tsarin mulkin Najeriya sun kare su daga muzgunawa daga hukuma a dukkan kasashe kuma a Najeriya ma bai kamata abun ya zama daban ba.

Lauyan haka zalika ya bayyana a cikin wasikar tasa cewa a matsayin sa na mai rajin kare hakkin dan adam ya dauki alkawarin kare yan gudun hijirar kuma zai cigaba da bin kadin hakkokin su.

A wani labarin kuma, 'Yan majalisar jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan a ranar Laraba sun amince da karin wa'adin mulki ga dukkan shugabannin kananan hukumomin ta 14 har na tsawon karin wata daya.

A baya ma dai majalisar ta jihar ta karawa shugabannin kananan hukumomin wa'adin watanni uku bayan sun shafe shekara uku na wa'adin mulkin su na farko a watan Jarairun da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel