Jihar Niger za ta kashe N3.2bn wajen gyara gidan gwamnati

Jihar Niger za ta kashe N3.2bn wajen gyara gidan gwamnati

- Jihar Niger za ta kashe naira biliyan 3.2 wajen gyara gidan gwamnati

- Kwamishinan ayyuka, Zakari Jikantoro ya bayyana cewa an raba aikin ne a rukuni biyu, inda na farko ya ci naira biliyan 2.1, sannan na biyu zai ci naira biliyan 1.6

- Yace rukuni na biyun zai kama daga ginin saukar baki uku mai dauke da dakuna uku-uku, wajen wanka na shakatawa, da sauransu; yayinda rukuni na farko ya danganci gidan gwamnati, kofar gaba da kuma Katanga

Gwamnatin jihar Niger tace kudaden da za a kasha wajen gyare-gyaren gidan gwamnatin jihar zai kai kimanin naira biliyan 3.2.

Kwamishinan ayyuka, Zakari Jikantoro ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna, babbar birnin jihar a jiya Alhamis, 21 ga watan Maris.

Yace ayyukan an raba su ne a rukuni daban-daban, inda ya kara da cewar an kammala aiki akan rukunin farko wanda ya ci kimanin naira biliyan 2.1; yayinda aka bayar da kwangilan na biyu wanda ya kai kimanin naira biliyan 1.6.

Jihar Niger za ta kashe N3.2bn wajen gyara gidan gwamnati
Jihar Niger za ta kashe N3.2bn wajen gyara gidan gwamnati
Asali: Depositphotos

Yace rukuni na biyun zai kama daga ginin saukar baki uku mai dauke da dakuna uku-uku, wajen wanka na shakatawa, da sauransu; yayinda rukuni na farko ya danganci gidan gwamnati, kofar gaba da kuma Katanga.

KU KARANTA KUMA: Dogara ya bankado wani shiri da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin yi

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a ranar Alhamis sun yiwa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, isgili kan kokarin kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari a kotu.

Atiku ya lashi takobin cewa sai ya kwace kujeran shugaba Muhammadu Buhari a kotu bisa ga rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Febrairu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel