Gwamnatin tarayya ta rufe kes din karar da ta shigar da tsohon alkalin alkalai, Onnoghen

Gwamnatin tarayya ta rufe kes din karar da ta shigar da tsohon alkalin alkalai, Onnoghen

Da alama dai karar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar tana tuhumar tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai shari'a Walter Onnoghen bisa zargin mallakar dukiyar haram ta zo karshe biyo bayan rufe kes din da bangaren masu kara suka yi.

Majiyar mu dai ta Jaridar ThisDay ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bukaci a rufe kes din biyo bayan sabani tare da cin karo da juna da shaidun da suka gabatar a karar suka rika yi a gaban alkalin kotun da'ar ma'aikata inda ake shari'ar.

Gwamnatin tarayya ta rufe kes din karar da ta shigar da tsohon alkalin alkalai, Onnoghen
Gwamnatin tarayya ta rufe kes din karar da ta shigar da tsohon alkalin alkalai, Onnoghen
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yar Arewa ta samu mukamin kasa-da-kasa

Shi dai Mai shari'a Onnoghen idan mai karatu bai manta ba ana tuhumar sa ne da laifin kin bayyana ainihin gaskiyar kadarorin sa ba da kuma tara kudaden da suka wuce misali da ake kyautata zaton na haram ne.

A saboda haka ne ma wata kungiya dake rajin tabbatar da shugabanci na gaskiya suka rubuta takardar koke ya zuwa kotun da'ar ma'aikata ta kasa watau Code of Conduct Tribunal (CCT) kafin daga bisani a soma tuhumar sa.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar nan dake yaki da masu cin hanci da rashawa ta tarayyar Najeriya watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) na rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya bukaci a kirkiro wasu sabbin dokoki masu tsauri kan masu satar mai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel