Zaben raba gardama: Za a takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa a Kano ranar Asabar

Zaben raba gardama: Za a takaita zirga-zirgan mutane da ababen hawa a Kano ranar Asabar

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta takaita zirga-zirgan motoccin hawa, a daidaita sahu da sauran ababen hawa a kananan hukumomi 44 da ke jihar.

A cewar rundunar 'yan sandan, an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben raba gardama na gwamna da za ayi a ranar 23 ga watan Maris lami lafiya.

Zaben raba gardama a Kano: An takaita zirga-zirgan al'umma da ababen hawa
Zaben raba gardama a Kano: An takaita zirga-zirgan al'umma da ababen hawa
Asali: UGC

Wannan sakon yana kunshe ne cikin wata sanarwar da ta fito daga hannun jami'in hulda da al'umma na rundunar, DSP Abdullahi Haruna a yau Alhamis.

DUBA WANNAN: 'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

Abdullahi ya ce ba za a bari al'umma suyi amfani da ababen hawa ba daga karfe 6 na safiya zuwa 6 na yammacin ranar da za a gudanar da zaben.

Ya shawarci dukkan masu zuwa kada kuri'u su taka da kafa zuwa rumfunan zaben da za su kada kuri'unsu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel