Shugaban majalisa da Kakaki: Duk wanda Buhari da Oshiomole ke so za'a zaba

Shugaban majalisa da Kakaki: Duk wanda Buhari da Oshiomole ke so za'a zaba

Tsohon Ministan Sufuri, Cif Ebenezer Babatope, ya ce shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, ne zasu zabi wanda zai zama shugaban majalisar dattawa, da kakakin majalisar wakilai.

Yayinda yake hira da jaridar Independent, Babatope wanda ya siffanta Oshiomole matsayin mai taurin kai ya ce tunda APC ke da rinjaye a majalisun guda biyu, jam'iyyar ce zata gabatar da shugabanninta amma Buhari da Oshiomole zasu darje.

Yace: "A kan shugabancin majalisar dokokin tarayya, wannan aikin mambobin jam'iyyar ne idan suka yarda, saboda APC ke da rinyaye a majalisar dattawa da wakilai.

"Amma duk mun san Buhari sai abinda ya ga dama zai yi, saboda yana iya hakan. APC kuma na da shugaba mai taurin kai, Adams Oshiomole."

"Duk wanda Buhari da Oshiomole suke so zai iya hawa kujeran amma da ikon Allah, idan aka kammala kareye-kareye a kotun zabe, kasar nan zata samu cigaba."

KU KARANTA: Rikicin Limancin na neman raba kan al'ummar jiha, gwamna ya yi gargadi

Mun kawo muku rahoton cewa manyan ‘Yan siyasa da kuma ‘Yan majalisun da su ka fito daga yankin Arewa maso gabas da kuma Arewa ta tsakiya sun matsa lamba cewa su za su fito da shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘Yan majalisan yankunan Arewa ta tsakiya da gabas sun tasa jam’iyyar APC mai mulki a gaba domin a ba su damar tsaida wanda zai jagoranci ragamar majalisar dattawan kasar a majalisa ta 9.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel