Sake zabe: IGP ya tura manyan jami’ai 23 domin sanya idanu a mazabu a fadin kasar

Sake zabe: IGP ya tura manyan jami’ai 23 domin sanya idanu a mazabu a fadin kasar

Mukaddashin Shugaban yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya umurci mataimakin sufeto janar na yan sanda da kuma kwamishinonin yan sanda a jihohin da za a sake zabe da su tabbattar da cewar an shirya abubuwan da ya kamata wajen tabbatar da kariya a wuraren da za a gudanar da zabuka.

Domin kara karfafa tsaro a wuraren zaben, IGP ya tura manyan jami’ai wadanda suka hada da DIG guda biyar, AIG uku da kuma Karin CP guda goma sha biyar domin sanya idanu, da kuma tallafa wa jami’an tsaro da ke kasa a wadannan jihohi.

Daga cikin kwamishinoni 15 da aka kara an tura uku zuwa jihar Benue, uku zuwa Sokoto, biyu zuwa Adamawa, biyu zuwa Bauchi, biyu zuwa Kano sannan biyu zuwa jihar Plateau. Hakazalika an tura guda daya zuwa jihar Imo.

Sake zabe: IGP ya tura manyan jami’ai 23 domin sanya idanu a mazabu a fadin kasar
Sake zabe: IGP ya tura manyan jami’ai 23 domin sanya idanu a mazabu a fadin kasar
Asali: Original

Yayinya yake yaba ma jami’an akan rawar ganin da suka taka a zabukan baya, shugaban yan sandan ya bukaci sauran da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu a lokacin zabe.

KU KARANTA KUMA: Dogara ya bankado wani shiri da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin yi

Ya gargadi yan siyasa da kada su taka ka’idar zabe ta hanyar aikata munanan ayyuka kamar kwace akwatunan zabe, siyan kuri’u da tayar da rikici, inda ya kara da cewa duk wanda ya taka doka zai fuskanci hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel