Rikicin Limancin na neman raba kan al'ummar jiha, gwamna ya yi gargadi

Rikicin Limancin na neman raba kan al'ummar jiha, gwamna ya yi gargadi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya gargadi kawo rikici yayin gudanar da Sallah da ayyukan Ibada a babban Masallacin Benin, babbar birnin jihar Edo.

Gwamnan ya yi wannan gargadi ne ranar Alhamis yayin ganawa da shugabannin Musulman jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar, Hanarabul Kabiru Adjoto, da Sarkin Auchi, Alhaji Aliru Momoh, Ikelebe III.

Ya ce yana sane da rikicin shugabancin babbar Masallacin Benin tsakanin Alhaji Jamiu Edosomwan da Alhaji Fatai Enabulele, amma ya ki sanya baki ne saboda yana kyautata zaton zasu sulhunta kansu.

Yace: "A matsayinmu na gwamnati, mun san abinda ke faruwa, mun san kalubalen da rikicin a matsayin rikicin cikin gida da ake bukatar su sulhunta tsakaninsu. Da rasuwar Alhaji Edosomwan, ya kamata ace a sulhunta juna amma na ji kunya rikicin ya cigaba. Amma ina farin ciki yanzu anyi sulhu."

"Zan sanar da diraktan hukumar DSS su samar da isasshen tsaron a babbar Masallacin Benin domin dakile masu kawo rikici."

"Bari in gargadeku cewa duk wanda ya kawo tangarda kan ayyukan ibada a Masallaci zai fuskanci fushin hukuma"

A bangare guda, dubunnan jama'a sun halarci Sallar Juma'a a gaban Masallacin da aka hallaka Musulmai 50 a kasar Nuzilan farkon makon nan. Firam Ministan kasar, Jacinda Arden, ya gabatar da gajeren jawabi har ya kawo hadisin Annabi (SAW).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel