Dogara ya bankado wani shiri da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin yi

Dogara ya bankado wani shiri da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin yi

Kakakin majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara, ya sanar da Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, da sauran hukumomin tsaro kan wani zargin makirci da gwamnatin jihar Bauchi ke kulla masa domin shafa masa kashin kaza akan wani laifi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Dogara, Turaki Hassan yayi a jiya Alhamis, 21 ga watan Maris.

A cewar sanarwar, kakakin majalisan a wasika mai kwanan wata 21 ga watan Maris, 2019, zuwa ga Sufeto Janar na yan sanda wanda aka yi kwafin Darakta Janar na DSS, yace ya samu bayanai abun dogaro na wani makirci da ake shirin kulla masa da hujjojin karya ta hanyar yiwa Babura da motocin fenti da logon jam’iyyarsa (PDP) da kuma hotunansa, wanda za a yi amfani da su wajen aikata laifuka da kuma shafa masa kashin kaza.

Dogara ya bankado wani shiri da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin yi
Dogara ya bankado wani shiri da gwamnatin jihar Bauchi ke shirin yi
Asali: Twitter

Yace: “Na rubuta wannan wasika don sanar Sufeto Janar na yan sanda cewa na samu bayanan kwararru game da wani makirci da gwamnatin jihar Bauchi ke yin a sanya ni cikin wani laifi.

“Gwamnatin jihar Bauchi ta tanadi daruruwan ababen hawa, wanda za a yi wa fenti da hotuna na da logon PDP da kuma sunana.

KU KARANTA KUMA: Mukkadashin Shugaban alkalan Najeriya ya rantsar da sabbin mambobin kotun zabe 13

“Shirin shine cewa gwamnatin jihar za ta nemi wasu yan ta’adda sannan ta ababen hawan wanda za su yi amfani da su wajen aikata laifuka sannan daga bisani su barsu a wajen don shaafa mani bakin fenti.

“Da wannan wasikar na ke sanar day an sanda da sauran hukumomin tsaro domin su zuba idanu sosai akan wadannan yan ta’addan da gwamnatin Bauchi ke shirin yadawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel