Mukkadashin Shugaban alkalan Najeriya ya rantsar da sabbin mambobin kotun zabe 13

Mukkadashin Shugaban alkalan Najeriya ya rantsar da sabbin mambobin kotun zabe 13

- Mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya, Justis Ibrahim Tanko Muhammed ya rantsar da akalla mambobin kotun sauraron kararrakin zaben 13

- Justis Tanko ya bukaci alkalai da su kasance masu kyawawan halayya sannan su jajirce, domin a yanzu kallo ya koma kansu don ganin sun yi adalci ba tare da yin alfarma ko son kai ga wani ba

- Ya ja hankalinsu kan yanayin rantsuwar da suka dauka, inda ya kara da cewa yanzu akwai wani alkawari tsakaninsu da mahaliccinsu

Mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya, Justis Ibrahim Tanko Muhammed ya rantsar da akalla mambobin kotun sauraron kararrakin zaben 13 a jiya, Alhamis, 21 ga watan Maris a kotun koli.

Mambobin sune; Justis A.O. Onovo, Justis R.O. Odugu, Justis S.B. Belgore, Justis T.A.O. Oyekan-Abullai, Justis A.J. Coker, da kuma Justis E.I. Oritsejafor. Sauran sune Justis C. Okoh, Justis O.S. Olusanya, Justis C.A. Ononeze-Madu, Justis P.U. Nnodum da kuma Justis J.C.L. Okibe.

Mukkadashin Shugaban alkalan Najeriya ya rantsar da sabbin mambobin kotun zabe 13
Mukkadashin Shugaban alkalan Najeriya ya rantsar da sabbin mambobin kotun zabe 13
Asali: Facebook

A halin da ake cikim mambobi biyu wadanda suka hada da, Justis O. Kasali da Justis M.O. Obadina basu samu damar halartan taron ba.

Da farko a jawabinsa, mukaddashin Shugaban alkalan ya bukaci alkalai da su kasance masu kyawawan halayya sannan su jajirce, domin a yanzu kallo ya koma kansu don ganin sun yi adalci ba tare da yin alfarma ko son kai ga wani ba.

Ya ci gaba da jan hankalinsu kan yanayin rantsuwar da suka dauka, inda ya kara da cewa yanzu akwai wani alkawari tsakaninsu da mahaliccinsu, yayinda yace babu wani kafa da za a bayar na rashin yin abunda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Kwamishinan 'yan sandan Kano bai san aikinsa ba — Ganduje

Da yake ci gaba da jawabi, Justis Tanko ya sanar da sabbin mambobin kotun cewa an bincike su sosai sannan daga bisani aka zabi jaruman alkalai a kasar wadanda suka cancanci wannan aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel