Kwamishinan yan sandan Kano ya ba kungiyar lauyoyin Najeriya hakuri akan tsare mambobinta

Kwamishinan yan sandan Kano ya ba kungiyar lauyoyin Najeriya hakuri akan tsare mambobinta

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Muhammed Wakili a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris ya ba kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar hakuri akan zargin kai hari da cin mutuncin wasu lauyoyi a jihar.

Wakili, ya ba da hakurin ne a lokacin da ya ziyarci hedkwatar kungiyar da ke a yankin Farm Centre agarin Kano.

Kwamishinan ya bayyana cewa lauyoyi abokan ci gabansu ne don haka ya yanke shawarar ba kungiyar hakuri domin kore gaba.

Kwamishinan yan sandan Kano ya ba kungiyar lauyoyin Najeriya hakuri akan tsare mambobinta
Kwamishinan yan sandan Kano ya ba kungiyar lauyoyin Najeriya hakuri akan tsare mambobinta
Asali: UGC

“Lauyoyi abokan aikina don haka ina fatan za mu ci gaba da aiki tare sannan mu yi abunda ya kamace mu daidai da doka,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa a shirye yake day a bai wa kungiyar hakuri ta kowace hanya da mambobin kungiyar suke so imma a rubutacciyar wasika ko kuma ta kafofin watsa labarai.

Da yake martani akan haka, Shugaban kungiyar a jihar, Musa Abdullahi-Lawal yayi godiya ga kwamishinan yan sandan kan ziyarar da yayi masu.

KU KARANTA KUMA: Akwai alaka mai kyau a tsakanina da Ganduje – CP Wakili

Ya kuma nuna shirin kungiyar da yin aiki tare da yan sanda a jihar domin tabbatar da adalci cikin gaggawa.

A ranar Laraba ne kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar sukaa ba rundunar yan sandan jihar sa’o’i 48 wanda a ciki ta bukacci ta bai kungiyar hakuri a bainar jama’a kan zargin tozarta mambobinta a hanyarsu ta gudanar da aikinsu na doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel