Atiku fa kawai bannatar da kudinsa zai yi a kotu - Gwamnonin jihar Neja da Edo suna isgili

Atiku fa kawai bannatar da kudinsa zai yi a kotu - Gwamnonin jihar Neja da Edo suna isgili

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a ranar Alhamis sun yiwa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, isgili kan kokarin kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari a kotu.

Atiku ya lashi takobin cewa sai ya kwace kujeran shugaba Muhammadu Buhari a kotu bisa ga rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Febrairu, 2019.

KU KARANTA: INEC ta sanar da ranar da sabbin gwamnoni zasu karbi takardar shaidar nasarar zabe

Obaseki da Bello shin Atiku ba ya cikin hayacinsa ne lokacin da yayi ikirarin cewa ya lallasa Buhari da kuri'u 1.6m a zaben.

Sun yi wannan magana ne a lokaci daban-daban ga manema labaran fadar shugaban kasa dake Abuja.

Obaseki yace: "Kun ji abinda aka ce, basu cikin hayacinsu."

Shi kuma gwamnan jihar Neja ya baiwa Atiku shawara kada yayi asarar kudinsa saboda kotu ba zata bashi nasara ba.

Kana ya kara da cewa masu tuntsura Atiku ya kalubalanci nasarar Buhari a kotu kudinsa kawai suke son ci.

A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa ga dukkan alamu, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Alhaji Atiku Abubakar, sun shiga wani bala'in dimuwa sakamakon fadin da sukayi a zabe.

APC ta bayyana hakan ne yayinda take martani kan ikirin PDP cewa dan takararta, Atiku Abubakar, ya lallasa shugaba Muhammadu Buhari da kuri'u miliyan daya da dubu dari shida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel