INEC ta sanar da ranar da sabbin gwamnoni zasu karbi takardar shaidar nasarar zabe

INEC ta sanar da ranar da sabbin gwamnoni zasu karbi takardar shaidar nasarar zabe

Hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta wato INEC ta sanar da cewa wadanda suka samu nasara a zaben gwamnonin da aka kammala a fadin tarayya zasu karbi takardar shaidar nasararsu ranar Laraba, 27 ga watan Maris da Juma'a 29.

Kwamishanan hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yada labarai, Festus Okoye, ya alanta hakan ne a ranar Alhamis a birnin Abuja yayinda yake hira da manema labarai kan yadda abubuwa ke gudana fame zabubbukan da ba'a kammala ba.

Wannan yana nuni ga cewa cikin jihohi 29 da gudanar da zabe ranar 9 ga watan Maris, 22 kadai zasu karbi takardar shahadar yayinda sauran bakwai suna sauraron umurnin kotu kan shin za'a cigaba ne ko kuma za'a sake zaben gaba daya.

KU KARANTA: Shekarau ya ciri tuta ta samun yawan adadin kuri'u a zaben bana

Yayinda aka dakatad da zabe a jihar Rivers, an gaza samun zakara a jihohi shida wanda ya kunshi Bauchi, Adamawa, Benue, Plateau, Sokoto da Kano.

Yace: "Za'a gabatar da takardun shaidar nasara ga sabbin gwamnoni kuma kwamishanonin hukumar ne zasuyi hakan tsakanin ranar Laraba, 27 da Juma'a 29 ga watan Marsi, 2019."

Ya ce shugabannin hukumar INEC a jihohin daban-daban zasu sanar da ranar a za'a gabatar da takardu a kowace jiha bayan tuntubar kwamishanonin.

Kana ba da dadewa ba za'a sanar da ranar gabatar da wannan takardar shahada ga wadanda sukayi nasara a zaben kujerun majalisun dokokin jiha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel