Kwamishinan 'yan sandan Kano bai san aikinsa ba — Ganduje

Kwamishinan 'yan sandan Kano bai san aikinsa ba — Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi tsokaci akan alakar da ke tsakaninsa da kwamishinan yan sandan jihar, CP Muhammed Wakili, inda ya bayyana cewa alaka ce ta aiki ta hada su.

Har ila yau Ganduje ya kalubalanci salon tsarin Shugabancin Wakili da kuma kamun ludayinsa akan aiki.

A hira da Ganduje yayi da shafin BBC Hausa yace: "Alaka ta da shi alaka ce ta aiki taa hada ni da shi, ban san shi ba kafin wannan lokaci amma na kamun ludayinsa akwai ayar tambaya kwarai da gaake a tattare dashi, kamar yadda ake gani mutane da dama na ganin yana da alaka wato ya dau bangare a wannan harka ta siyasa.

"Abu na biyu ina ganin yana yi wa aikinsa rikon sakainar kasha, domin za ka ga abubuwa da yawa da ya kamata ya sa ido ya jajirce a kansu, bai sa ba, kuma dadin abun shine ita kanta hedkwatarsu ta tsaro sun san da wannan, kuma ina ganin idan bai canja rawarsa bat oh ina ganin yana da matsala."

Kwamishinan 'yan sandan Kano bai san aikinsa ba — Ganduje
Kwamishinan 'yan sandan Kano bai san aikinsa ba — Ganduje
Asali: Depositphotos

Da aka tambaye shi ko sun kai korafi ga shugabanninsa da ke sama, Gwamnan yace: “Bamu kai korafi ba amma alúmma daban-daban wato kungiyoyi masu zaman kansu sun riga sun kai shi kara akan wannan. Sun kuma rubuta, ka ga kamar yadda yasa aka kama mataimakin gwamna, karya ne ba kubutar dashi suka yi ba, sun kama shi ne, abunda ya faru yan jam’iyyar APC da yawa sun taru sun je wannan wuri, aka je aka bashi labara sai ya sa masu tiya-gas suka gudu, da suka gudu ba asani baa she ya je ya tara yan jam’iyyar PDP suka je suka taro, don haka shi mataimakin gwamna da yaji ana yamutsi da jam’iyyar APC sai yaje ya ga me yake faruwa, toh saboda haka sai ya je ya shiga cikin rundunar yan jam’iyyar PDP wanda suka yi masa ihu, suna yi masa chaa cewa bama yi da sauransu, wanda yake dama siyasa ta gaji wannan.

“Saboda haka shi kuma kwamishinan yan sanda sai yayi amfani da wannan dama yace wai yana tserar da shi, toh idan yana tserar da shi ya kai shi gidansa mana ko ya kawo shi ofis amma sai ya tafi da shi ofishin yan sanda wanda yake ba shi da iko yayi haka. Da gwamna da mataimakin gwamna na da kariya da tsarin mulki ya bayar, saboda haka wannan na daga cikin dalilin da yasa nace bai san aikinsa ba sosai."

KU KARANTA KUMA: Akwai alaka mai kyau a tsakanina da Ganduje – CP Wakili

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili ya bayyana matsayarsa akan siyasa, inda ya bayyana cewa sh baya goyon bayan kowani bangare na siyasa.

CP Wakili ya jadadda cewa amana ne ce babba aka damka masa sannan kuma yae aikinsa shine ya kare al’umma da dukiyoyinsu baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel