Akwai alaka mai kyau a tsakanina da Ganduje – CP Wakili

Akwai alaka mai kyau a tsakanina da Ganduje – CP Wakili

- Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Muhammed Wakili ya bayyana matsayarsa a harkar siyasa inda yace baya goyon bayan kowani bangare

- CP Wakili ya kuma bayyana cewa akwai kyakyawar alaka a tsakaninsa da Gwamna Ganduje, inda yace yana kuma bashi goyon baya dari-bisa-dari akan aikinsa

- Wakili ya kuma jadadda cewa aikinsa amana ce da kuma tabbatar da kare al'umma da dukiyoyinsu

A daidai lokacin da ake shirin sake zaben gwamna a jihar Kano a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Muhammed Wakili ya bayyana matsayarsa akan siyasa, inda ya bayyana cewa sh baya goyon bayan kowani bangare na siyasa.

CP Wakili ya jadadda cewa amana ne ce babba aka damka masa sannan kuma yae aikinsa shine ya kare al’umma da dukiyoyinsu baki daya.

Kwamishinan yayi wannan tsokaci ne a wata hira da yayi da shafin BBC Hausa, a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Akwai alaka mai kyau a tsakanina da Ganduje – CP Wakili
Akwai alaka mai kyau a tsakanina da Ganduje – CP Wakili
Asali: UGC

Ya kara da cewa idan har yabi bayan bangare guda a siyasa toh babu shakka yayi zalunci, yace shi kowa nasa ne domin baya son zalunci.

Daga nan, CP Wakili ya yi tsokaci kan dangantakarsa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje inda ya ce akwai kyakkayawar alaka a tsakaninsu.

"In aiki ya taso yana nema na mu yi shawara kuma yana ba ni goyon baya 100 bisa 100".

KU KARANTA KUMA: Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna

A halin da ake ciki kwamishinan na jihar Kano na daf da yin ritaya daga aiki domin a watan Mayun wannan shekarar zai kammala aikin nasa.

Ya kuma bayyana cewa a ce shirye yake ya karbi duk wani mukami idan gwamnati ta yi sha'awar ba shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel