An sake kai hari kan wasu Masallatai a Ingila

An sake kai hari kan wasu Masallatai a Ingila

An kai wani hari a wasu rukunin masallatai da ake kira ‘MFive’ a birnin Birmingham dake kasar Ingila kamar yadda ‘yan sanda suka tabattar a ranar Alhamis.

Wannan harin da aka kai zuwa ne bayan wani harin da wani wani dan bindiga ya kai a wani masallacin kasar New Zealand dake yankin Christchurch, inda ya kashe mutane 60.

Jami’an ‘yan sanda a West Midlands sun bayyana cewar suna gudanar da bincike a kan harin da aka kai masallatan na Birmingham inda aka lalata tagogin su.

‘Yan sandan sun bayyana cewar sun isa rukunin masallatan ne bayan samun rahoton cewar wani mutum na fasa tagogi da guduma.

Kazalika sun bayyana cewar jami’an ‘yan sanda dake makobtaka da rukunin masallatan na aiki wakilan masallatan dake yankin domin tabbatar da tsaro.

An sake kai hari kan wasu Masallatai a Ingila
Wani Masallaci a Turai
Asali: Depositphotos

Tun bayan harin da aka kai masallacin Christchurch a kasar New Zealand jami’an mu dake ofishin West Midlands ke aiki da shugabannin wuraren ibada dake yankin.

“Mun basu tabbacin samar da tsaro a masallatai da coci da wuraren ibada,” a cewar jami’in dan sanda, Dave Thompson.

DUBA WANNAN: Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna

Sannan ya cigaba da cewa, “ya zuwa yanzu ba zamu iya cewa ga dalilin kai harin ba. Wannan lokaci ne da ya kamata dukkan jama’a su hada kai domin nuna kyama ga duk ma su son haifar da gaba da cusa tsoro a zukatan jama’a."

Shabana Mahmood, mamba a majalisa daga Birmingham, ya ce bai ji dadin labarin kai harin ba tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalin su tare da yin kira gare su da su bawa jami’an ‘yan sanda duk wani bayani da kan iya taimaka wa biciken su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel