Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna

Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammed Wakili, da ake yiwa lakabi da ‘Singham’ ya ziyarci mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a fadar sa.

Ziyarar kwamishina Singham na zuwa a daidai lokacin da ya rage kwana daya kacal a gudanar da zaben raba gardama a matakin gwamna a wasu mazabu dake kananan hukumomin jihar Kano 12.

Ranar Asabar, 23 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar domin gudanar da zaben raba gardama a wasu jihohi 6, ciki har da jihar Kano.

Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna
Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II
Asali: Facebook

Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna
Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili da Sarki Sanusi II
Asali: Facebook

Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ ya ziraci Sarki Sanusi II, hotuna
Kwamishinan ‘yan sanda Muhammed Wakili ‘Singham’ a fadar Sarki Sanusi II
Asali: Facebook

Ba a bayyana dalilin ziyarar kwamishina Singham zuwa fadar sarkin Kano ba. A kwanakin baya ne aka ji mai martaba Sarki Sanusi II na yabon kwamishinan bisa irin yadda ya ke aiki ba sani-ba-sabo domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Ina da tawakkali, zan rungumi kaddara idan na fadi zabe – Ganduje

Sai dai jam’iyyar APC a jihar Kano ta zargi kwamishina Singham da nuna goyon baya ga jam’iyyar PDP a zaben gwamn da INEC ta gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel