Shugaba Buhari bayyar da haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu

Shugaba Buhari bayyar da haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayar da karin haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu inda yace zai gudanar da gwamnatin sa ne a faifai kuma wadda zata tabbatar da adalci ga kowa.

Haka ma dai shugaban kasar wanda ya doke dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar da ya gabata, ya ce wa'adin mulkin sa zai mayar da hankali sosai a fannin tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.

Shugaba Buhari bayyar da haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu
Shugaba Buhari bayyar da haske akan irin gwamnatin da zai yi wa'adin sa na biyu
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kara wa'adin mulkin Ciyamomi a Zamfara

Shugaban kasar dai yayi wannan karin hasken ne yayin da yake jawabi yayin ziyarar da shugabannin kungiyar 'yan jarida ta kasa watau Nigerian Union of Journalists (NUJ), karkashin jagorancin Mista Chris Isiguzo suka kai masa a fadar sa.

Haka zalika ma dai shugaban kasar ya roki dukkan 'yan jaridar da su ba gwamnatin sa hadin kai musamman wajen wayar da kan al'ummar kasar akan ayyun cigaban kasa da zaman lafiyar ta.

Su ma da suke jawabin godiya shugabannin kungiyar sun ba shugaban kasar tabbacin yin aiki kafada-da-kafada da gwamnatin sa wajen yin dukkan abubuwan da ya kamata kamar yadda doka ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel