Ina da tawakkali, zan rungumi kaddara idan na fadi zabe – Ganduje

Ina da tawakkali, zan rungumi kaddara idan na fadi zabe – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shi mai tawakkali ne ga ubangiji, a saboda haka zai rungumi kaddara matukar ya fadi zaben gwamna da za a maimiata a wasu mazabun jihar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Da yake amsa tambayoyin gidan jaridar sashen Hausa na BBC, Ganduje ya ce, “bani da wata fargaba, domin da karfin Allah zamu ci zabe kuma duk irin kura-kuran da aka samu makonni biyu da suka wuce yanzu an shawo kan su. Jami’an tsaro zasu tsaya su yi aiki sosai domin muna da kyakyawan zaton cewsar sun yi shiri sosai wannan karon.”

Da aka tambaye shi ko zai amince da sakamakon zabe?, sai Ganduje ya ce, “ai ka sani ni tuntuni nake cewa ‘tawakkaltu alallah, la haula wala kuwata illa billahil azim’ saboda haka na dogara da Allah kuma idan wani ya ci zabe ba ni ba, ‘Allah ya kiyaye faruwar hakan’, ni zan taya shi murna kuma zan karbi sakamakon da hannu biyu.

Sai dai yayin da Ganduje ke wadannan kalamai, jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, da dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar PDP, Abba Kabir Yusuf, sun bayyana cewar sun fasa kai ziyara mazabar Gama dake karamar hukumar Nasarawa kamar yadda suka yi niyya.

Ina da tawakkali, zan rungumi kaddara idan na fadi zabe – Ganduje
Ganduje
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar Kwankwaso da Abba sun fasa kai ziyara mazabar ne bayan samun bayanan sirri cewar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya tura ‘yan daba domin su kai hari a kan tawagar yakin neman zaben PDP idan sun shiga unguwar.

DUBA WANNAN: INEC ta saka lokacin tattara wa da sanar da sakamakon zaben jihar Ribas

Majiyar ta kara da cewa an tura ‘yan daba mazabar domin tayar da fitina da za a fake da ita wajen nuna gazawar kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammed Wakili, na tabbatar da tsaro a jihar.

Wata majiyar ta bayyana cewar dandazon jama’a daga mazabar ta Gama na turuwar kai ziyara gidan Kwankwaso domin nuna goyon bayansu ga dan takarar sa a zaben gwamna da za a maimaita ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel