Gwamnatin Buhari ta kaddamar da garambawul akan matatan mai na Fatakwal

Gwamnatin Buhari ta kaddamar da garambawul akan matatan mai na Fatakwal

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da gyare gyare tare da garambawul a matatar man fetir na garin Fatakwal dake jahar Ribas a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar man fetir na Najeriya, Dakta Maikanti Baru ne ya bayyana haka a garin Fatakwal yayin kaddamar da aikin, inda yace makasudin fara aikin shine cika burin gwamnatin Najeriya na tace kashi 90 na man da ake amfani dasu a Najeriya.

KU KARANTA: NNPC ta bayyana adadin biliyoyin litan mai data tura sassan kasar nan

Matatar main a garin Fatakwal ne na farko da aka fara ginawa a Najeriya, a shekarar 1965, wanda aka gina shi don ya tace gangan danyen mai 60,000 a kullu yaumin, daga bisani aka sake gina wani a shekarar 1989 da zai tace gangan mai 150,000.

Kenan gaba dayansu zasu tace gangunan danyen mai 210,000 a kowanne rana idan har suna aiki dari bisa dari, wannan yasa matatar mai ta Fatakwal ta zamto matatar mai mafi girma a Najeriya.

A jawbainsa, Baru ya bayyana cewa an bada kwangilar gyare gyaren ne ga kamfanin ENI da kuma kamfanin da suka fara gina matatar man a shekarar 1965, saboda sune suka san makaman aiki fiye.

“Tun shekarar 200 rabon da aka sake yi ma matatarman garambawul, don haka a wannan karon zamu kwance duk wani inji da ake amfani dashi, tare da duba duk wani tsare tsare aiki, daga nan mu mayar dasu idan muka kammala gyaransu.” Inji shi.

Daga karshe Baru yace ENI, Agip da kuma kuma kamfanin NNPC sun yi alkawarin samar ma Najeriya sabbin kayan aiki na zamani don kammala gyaran cikin lokacin da aka diba, idan ba haka ba sai a kwashe sama da watanni 36 kafin a samu injinonin daga kamfanonin da ake kerasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel