Cikamakin zabe: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin kulle iyakokin wasu jihohi 3

Cikamakin zabe: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin kulle iyakokin wasu jihohi 3

Gwamnatin tarayya ta umurce hukumar shiga da ficen Najeriya ta kulle iyakokin jihohin Adamawa, Benuwe, da Sokoto gabanin cikamakin zabe da za'a gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2019.

Ministan harkokin cikin gida, Laftanan Janar AbdulRahman Dambazau, ya bayyana hakan ne ta bakin kontrolan hukumar shiga da fice Najeriya, Muhammad Babandede, a Abuja, ranar Alhamis.

A cewarsa, za'a kulle iyakokin daga ranar Juma'a misalin karfe 12 na rana zuwa ranar Lahadi misalin karfe 12.

Ya bayyana cewa manufar hakan shine hana shiga da fice tsakanin jihohin da ke iyaka da wasu kasashe dake makwabtaka da Najeriya, saboda haka ana sanar da al'umma sun sani da kuma bin doka.

Za ku tuna cewa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayyana cewa za'a kammala zaben gwamnan jihohin Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Plateau da Sokoto sakamakon rashin samun zakara a zagayen farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel