Shugabancin majalisar dattawa: Dattawan Borno sun mara wa Ndume baya

Shugabancin majalisar dattawa: Dattawan Borno sun mara wa Ndume baya

- Dattawan jihar Borno sun nuna goyon bayansu ga Sanata Mohammed Ali Ndume game don ganin ya zamo Shugaban majalisar dattawa na gaba

- Sunce Ndume ya cancanci wannan matsayi domin jihar Borno ta bai wa APC mafi girman kaso na kurinta

- Jagoran wannan tafiya, Ambasada Dauda Danladi yace Ndume ne yafi cancantar wannan matsayi duba ga kasancewarsa a matsayin dan majalisa mai kokari kuma mai biyayya ga jam’iyyar

Manyan masu ruwa da tsaki daga jihar Borno sun nuna goyon bayansu ga Sanata Mohammed Ali Ndume game don ganin ya zamo Shugaban majalisar dattawa na gaba.

Ambasada Dauda Danladi wanda ya kasance jagoran wannan tafiya wacce ta hada da tsoffin gwanoni da ministoci da sauransu, yayi jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris a Abuja, inda yace Sanata Ndume na da abubuwan da ake bukata wajen jagoranci a majalisar dattawan, domin ganin ci gaban yan Najeriya.

Shugabancin majalisar dattawa: Dattawan Borno sun mara wa Ndume baya
Shugabancin majalisar dattawa: Dattawan Borno sun mara wa Ndume baya
Asali: UGC

Ambasa Danladi yace Sanatan ya cancanci wannan matsayi a majalisar dokokin kasar saboda jihar Borno ta ba APC sama da kaso 90 na kuri’un jihar a zaben da aka kammala kwanan nan.

Tsohon jakadan na Najeriya a Pakistan yace Ndume ne yafi cancantar wannan matsayi duba ga kasancewarsa a matsayin dan majalisa mai jajircewa kuma mai biyayya ga jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Abba da Kwankwaso suka fasa ziyarar mazabar Gama

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa anyi hayaniya sosai a zauren majalisar dattawa yayin zaman da akayi na yau Laraba 20 ga watan Maris a lokacin da ake tattaunawa a kan zargin da wasu keyi na cewa anyi amfani da sojoji fiye da kima a wasu jihohi yayin zaben 2019.

Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta Yamma a majalisar ne ya gabatar da kudirin zargin amfani da sojoji fiye da kima a lokacin zaben da kuma zargin fifiko da Hukumar Zabe INEC ta aikata a wasu johohin a cewarsa.

Wasu sanatoci bakwai da suka hada da Sanata Mao Ohabunwa (Abia ta Arewa), Samuel Anyanwu (Imo ta Gabas), Ahmed Ogembe (Kogi ta Tsakiya), Obinna Ogba (Ebonyi ta Tsakiya), Matthew Uroghide (Edo ta Kudu), Clifford Ordia (Edo ta tsakiya) Biodun Olujimi (Ekiti ta Kudu) duk sun goyi bayan Dino Melaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel