Yadda wani Likita ya yiwa matar aure mai jinya fyade a asibiti

Yadda wani Likita ya yiwa matar aure mai jinya fyade a asibiti

Wani Likita a asibitin gwamnati dake jihar Sokoto mai suna, Tijjani Faruk, ya tayar da hankalin jama'ar asibitin bayan tona asirin kansa cewa ya yiwa wata matar aure mai jinya fyade bayan tsira mata alluran barci.

A wata hira da jaridar Daily Nigerian tayi da mijin matar da abin ya auku da ita mai suna Alhaji Shehu, ya bayyana cewa wani abokinsa ne ya basu shawaran zuwa wajen Likitan yayinda aka gano tanada wasu kulli a mararta wanda akafi sani da "Fibroid".

Watanni bayan aikin tiyata da aka gudanar domin cireshi, sai Likitan ya kirashi a waya cewa yana bukatar ganin matarsa domin akwai wasu dube-dube da yake bukatan yi mata.

Yadda wani Likita ya yiwa matar aure mai jinya fyade a asibiti

Yadda wani Likita ya yiwa matar aure mai jinya fyade a asibiti
Source: Facebook

Karanta jawabinsa: "Ya kirani ranar Juma'a da rana inda ya bukaceni in turo uwargidata saboda ya gudanar da wasu dube-dube ranar Asabar misalin karfe 10 an safe, sai nayi abinda ya bukata. Ashe wani mugun abu yake shirin yi da iyalina."

"Yayinda ta tashi daga barci misalin karfe 7 na yamma ranar Asabar, sai ta gano cewa Dakta Tijjani Ahmad Faruq yayi lalata da ita yayinda ta fita daya hayacinta."

"Da ta tambayeshi meyasa yayi mata haka, bai bada wani dalili ba, innama hakuri ya rika bata na ta yafe masa."

"Yayinda ta tambayeshi wani magani zai bata domin hanata daukan juna biyu sakamakon abin yayi mata, sai yace ba zata sake iya haihuwa ba."

" Bayan wasu gwaje-gwaje da aka gudanar a asibitin Usmanu Danfodiyo da (UDUTH) da asibtiin Zafafi dake Sokoto, an gano cewa maimakon cire cutan dake jikinta kadai, ya dinke mata mahaifa kuma saboda haka, ba zata sake iya haihuwa ba."

" Tun ranar na lura matana ba ta zuwa asibiti duk yayinda na bukaceta taje. Daga karshe da ta bayyana min abinda ya faru, sai na umurceta ta sake komawa wajensa domin tona masa asiri ta hanyar daukan maganarsa a rediyo."

"Da ta fuskancesa kan shin meyasa yayi mata fyade, an dauki maganarsa a rediyo yana cewa idan ta fadawa mijinta, karshen aurenta kenan."

An kai kararsa wajen ma'aikatar kiwon lafiya kuma kwamishanan kiwon lafiyar jihar, Ali Inname, a ranar Alhamis ya tabbatar da cewa an nada kwamiti domin gudanar da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel