An kara wa'adin mulkin shugabannin kananan hukumomi 14 a Zamfara

An kara wa'adin mulkin shugabannin kananan hukumomi 14 a Zamfara

'Yan majalisar jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan a ranar Laraba sun amince da karin wa'adin mulki ga dukkan shugabannin kananan hukumomin ta 14 har na tsawon karin wata daya.

A baya ma dai majalisar ta jihar ta karawa shugabannin kananan hukumomin wa'adin watanni uku bayan sun shafe shekara uku na wa'adin mulkin su na farko a watan Jarairun da ya gabata.

An kara wa'adin mulkin shugabannin kananan hukumomi 14 a Zamfara
An kara wa'adin mulkin shugabannin kananan hukumomi 14 a Zamfara
Asali: Facebook

KU KARANTA: Farashin Naira ya fadi warwas a kasuwanni

Tun farko dai, Kakakin majalisar Alhaji Sanusi Rikiji shine ya karanto kudurin bukatar karin wa'adin wanda gwamnan jihar ta Zamfara, Abdul'aziz yari ya aikewa majalisar ta ofishin Sakataren gwamnatin jihar.

Takardar bukatar daga gwamnan jihar dai ta bayyana neman karin wa'adin a matsayin wani mataki da zai baiwa hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta Zamfara dama su kara shiryawa sosai kafin zaben.

A wani labarin kuma, Sabbin alkaluman kiwon lafiya na duniya sun nuna cewa kasar Najeriya a yanzu ita ce ta farko a jerin kasashen da suke fama da cutar kyanda inda alkaluma suka nuna cewa akalla yara a kasar sama da miliyan uku ne ba a yi masu rigakafin cutar ba a halin yanzu.

Shugaban dake kula da hukumar lafiya ta duniya watau World Health Organisation (WHO), a jihar Borno mai suna Dakta Audu Idawo shine ya bayya hakan a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar domin shirya tunkarar aikin rigakafin cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel