APC ta biya wasu manyan yan Najeriya don su roki Atiku da kada ya je kotu - Galadima

APC ta biya wasu manyan yan Najeriya don su roki Atiku da kada ya je kotu - Galadima

Kakakin kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa na PDP, Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bai wa wasu manyan yan Najeriya kudi, don su roki Atiku Abubakar da ya janye kudurinsa na zuwa kotu kamar yanda ya bayyana cewa APC ta yi amfani da rundunar soji wajen mirdiya a zaben shugaban kasa na 2019.

Yayinda Galadima yake magana a Channels Television a ranar Laraba, yace: “Hakika ko wani dan Najeriya a fadin duniyan nan wanda ya bi lamarin zaben 2019 a kasar yana sane da cewa anyi murdiya, gaskiya yan jam’iyyar APC sun yi fashi, sun yi amfani da jami’an tsaro musamman sojoji don yin murdiya,”

"Idan kuna ganin wannan zargi ne, ku je ku tambayi wurare da suka hada da Benue, Plateau, Borno, Yobe da Zamfara.

“A bari su tafi kotu, zan tabbatar da hakan. Kuna sane da cewa wata daya kafin zabe, rundunan soji ta bayyana aikinta mai taken Python Dance a fadin jihohi 36 dake kasar.”

APC ta biya wasu manyan yan Najeriya don su roki Atiku da kada ya je kotu - Galadima
APC ta biya wasu manyan yan Najeriya don su roki Atiku da kada ya je kotu - Galadima
Asali: UGC

“Wannan ya kasance daga shirye shiryen su da suka aiwatar a lokacin zabe kuma sunyi amfani da shi don razana masu zabe, su kashe masu zabe sannan su rubuta sakamakon zabe wa jam’iyyar APC. Wannan ne zargi? Ko baku ga abinda ya faru bane a rubuce rubuce dake bayyane don mu gani mun kuma san dan takaranmu ya lashe zaben nan kuma wannan ne yasa muka tafi kotu."

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakoki a jihohi 3

Galadima ya kara da cewa, “Jam’iyyar APC ta nace, ta kuma tallafa wajen zanga-zanga da kuma tallafa wa wassu jiga jigan yan Najeriya da kudi don mika roko ga Atiku da kada ya tafi kotu.

"Ina ruwan su? Dan takaran su a 2003, 2007, da 2011 bai tafi kotu ba domin kalubalantan sakamako? Ya taba taya wadanda suka lashe zabbuka a wannan lokacin murna?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel