Dalilin da ya sa Abba da Kwankwaso suka fasa ziyarar mazabar Gama

Dalilin da ya sa Abba da Kwankwaso suka fasa ziyarar mazabar Gama

Jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, da dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar PDP, Abba Kabir Yusuf, sun fasa kai ziyara mazabar Gama dake karamar hukumar Nasarawa kamar yadda suka yi niyya.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar Kwankwaso da Abba sun fasa kai ziyara mazabar ne bayan samun bayanan sirri cewar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya tura ‘yan daba domin su kai hari a kan tawagar yakin neman zaben PDP idan sun shiga unguwar.

Majiyar ta kara da cewa an tura ‘yan daba mazabar domin tayar da fitina da za a fake da ita wajen nuna gazawar kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammed Wakili, na tabbatar da tsaro a jihar.

Wata majiyar ta bayyana cewar dandazon jama’a daga mazabar ta Gama na turuwar kai ziyara gidan Kwankwaso domin nuna goyon bayansu ga dan takarar sa a zaben gwamna da za a maimaita ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Dalilin da ya sa Abba da Kwankwaso suka fasa ziyarar mazabar Gama
Abba da Kwankwaso
Asali: UGC

Wani jigo a Kwankwasiyya ya shaida wa majiyar mu cewar, “mun fasa ziyarar mazabar Gama kamar yadda muka yi niyya saboda mun samu labarin cewar gwamna Ganduje ya tura ‘yan daba zuwa unguwar domin su kai wa Kwankwaso hari tare da nuna gazawar kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammed Wakili."

DUBA WANNAN: INEC ta saka lokacin tattara wa da sanar da sakamakon zaben jihar Ribas

Mazabar Gama ce ma fi yawan masu kada kuri’a a zaben gwamna da za a maimaita a wasu mazabu a jihar Kano.

Mazabar na da masu rijistar zabe fiye da 47,000, wadanda ake ganin mafi yawansu magoya bayan jam’iyyar PDP ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel