Sake zabe: Jam’iyyar PDP ce za ta karbe Kano – Kwankwaso

Sake zabe: Jam’iyyar PDP ce za ta karbe Kano – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ce za ta lashe zaben da za a sake gudanarwa a jihar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta hannun mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Binta Spikin.

“Kwankwaso ya yarda da Kano sannan kuma ya damu sosai da makomar matasa, wadanda suka kasance abun kulawarsa a lokacin da yake a matsayin gwamnan Kano.

“Yayi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani labarin kafofin watsa labarai na kiyayya da aka alakanta da shi, musamman wadanda ke kokarin kawo hargitsi a jihar

Sake zabe: Jam’iyyar PDP ce za ta karbe Kano – Kwankwaso
Sake zabe: Jam’iyyar PDP ce za ta karbe Kano – Kwankwaso
Asali: UGC

“Sanata Rabiu Kwankwaso na kira ga mutanen jihar Kano, a fadin bangarorin siyasa, da su rike kansu cikin lumana a lokacin da suke zabar yan takara da suke muradi,” cewar Spikin yayinda take Magana a madadin Kwankwaso.

Ta kara da cewa: “Kwankwaso ya yarda da Kano sannan kuma ya damu sosai da makomar matasa, wadanda suka kasance abun kulawarsa a lokacin da yake a matsayin gwamnan Kano.

KU KARANTA KUMA: Mata 31 da Buhari zai yiwa nadin mukamai a sabuwar gwamnatin sa

“Yayi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani labarin kafofin watsa labarai na kiyayya da aka alakanta da shi, musamman wadanda ke kokarin kawo hargitsi a jihar.

“Sanatan ya yarda da cewar PDP ce za ta yi nasara a zabe na gaskiya da amana, kamar yadda ta yi a baya. Don haka,sake zabe ba zai dakile nasarar Abba Kabir Yusuf dan takarar jam’iyyar ba."

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel