Sake zabe: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakoki a jihohi 3

Sake zabe: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakoki a jihohi 3

- Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin jihohin Adamawa, Benue, da kuma Sokoto gabannin zaben da za a sake a ranar Asabar mai zuwa

- Za a rufe iyakokin ne daga maraicen ranar Juma’a, 22 ga watan Maris zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Maris

- Kudirin yin hakan shine domin hana zirga-zirga a iyakokin jihohin da abun ya shafa a lokacin zabe

Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakokin jihohin Adamawa, Benue, da kuma Sokoto gabannin zaben da za a sake a ranar Asabar, 23 ga watan Maris a jihohin.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana hakan a wata sanarwa dauke das a hannun kwanturola janar na hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, a Abuja a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

A cewarsa za a rufe iyakokin ne daga maraicen ranar Juma’a, 22 ga watan Maris zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Maris.

Sake zabe: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakoki a jihohi 3
Sake zabe: Gwamnatin tarayya ta yi umurnin rufe iyakoki a jihohi 3
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa kudirin yin hakan shine domin hana zirga-zirga a iyakokin jihohin da abun ya shafa a lokacin zabe.

“Ana bukatar jama’a da su lura sannan su tabbatar da hadin kai,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Zaben raba gardama: PDP ta bankado abinda Ganduje da APC ke kulla wa

Hukumar zabe mai zaman kanta dai ta sanya ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranakun sake zabe a jihohin Bauchi, Kano, Plateau, Sokoto da kuma Adamawa saboda kaddamar da zaben jihohin a matsayin ba kammalallu ba da hukumar tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel