Tsawa ta hallaka mutane 3 a jihar Delta

Tsawa ta hallaka mutane 3 a jihar Delta

Rundunar yan sanda reshen jihar Delta a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris ta bayyana cewa mutane uku ne suka mutu sanadiyar tsawa a yankin karamar hukumar Ugheli Uturu dake jihar.

Kwamishinan yan sanda jihar, CP Adeyinka Adele, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) inda yace har yanzu dai zato ne lamarin saboda babu rahoton likitoci dake nuna cewa tsawa ce sanadiyar mutuwar su.

An bayyana wadanda lamarin ya shafa a matsayin Matthew Utuama da Gabriel Djoma tare da wani makaniki da ya zo daga Onitsha don gyaran injinin motar tifa mallakar daya daga cikin mutane biyun da abun ya shafa.

Tsawa ta hallaka mutane 3 a jihar Delta
Tsawa ta hallaka mutane 3 a jihar Delta
Asali: Depositphotos

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 4:00 na rana a ranar Talata a Osieta Avenue, Otu-Jeremi a lokacin da ake ruwan sama wanda aka shafe tsawon mintuna 30 ana yi.

A cewar wani majiyi,mutane ukun sun kasance cikin wata gini a lokacin da abun bakin cikin ya faru, inda ya kara da cewa sun mutu nan take.

KU KARANTA KUMA: Zaben raba gardama: PDP ta bankado abinda Ganduje da APC ke kulla wa

“Sun kasance suna jiran ruwan sama ya yanke kafin saukar tsawa, an same su a mace a kasa bayan daya daga cikin wadanda suka ji rauni ya ja hankalin makwabta zuwa inda lamarin ya auku.

“Wanda ya samu raunin ya kasance dan rakiyan makanikin zuwa kauyen don gyaran mota.”

Majiyin ya ce, an kai gawawwakin Utuama da Djoma dakin ajiye gawa dake Babban asibitin Otu-Jeremi yayinda aka tafi da makanikin wanda ba a san asalinsa ba Onitsha don binnewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel