NNPC ta bayyana adadin biliyoyin litan mai data tura sassan kasar nan

NNPC ta bayyana adadin biliyoyin litan mai data tura sassan kasar nan

Hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC ta sanar da tura sama da litan mai biliyan biyu ta bututun mai zuwa sassa daban daban na kasar nan cikin shekaru biyu, daga shekarar 2016 zuwa yanzu, kamar yadda shugaban kamfanin kula da bututun main a Najeriya, NPSC, ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito shugaban kamfanin, Luke Anele ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 20 ga watan Maris yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, inda yace Najeriya nada isashshen man fetir da take turawa ta bututun mai.

KU KARANTA: Rashin Imani: Yadda wani mutumi ya kashe mai juna biyu bayan yayi mata fyade

“A kiyasi, mun tura sama da litan man fetir biliyan biyu tun daga fara aikin kamfanin nan, babban inda muke tara mai shine matattarar mai ta Mosimi, inda muke da karanci litan mai miliyan dari a koyaushe.

“Haka nan muna wasu matattaran da suka hada da Ibadan, Atlas Cove da kuma Aba, gaba daya litan mai miliyan dari biyu kenan a yanzu haka, baya ga wadanda suke cikin tankunanmu dake matatar mai ta Warri da Fatakwal.” Inji shi.

Anele ya koka kan yadda ake yawan fasa bututun mai, inda yace lamarin yafi aukuwa a tsakanin Aba zuwa Enugu, amma duk da haka yace suna gyarawa a duk lokacin da suka fahimci an fasa bututun mai.

A yanzu haka kamfanin ta dauki hayar wata kamfani na daban mai suna NETCO domin ta gudanar da bincike tare da gyara duk bututun da suka fashe, saboda idan aka samu ingantattun bututun mai, Najeriya zata rage asarar kudade da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel