Zaben raba gardama: PDP ta bankado abinda Ganduje da APC ke kulla wa

Zaben raba gardama: PDP ta bankado abinda Ganduje da APC ke kulla wa

- Jam' iyyar PDP babin jihar Kano ta zargi APC da Gwamna Ganduje da shirin hargitsa zaben da za a sake gudanarwa a jihar

- PDP ta kuma yi zargin cewa gwamnan na rabon kudi yana amsar katunan zaben mutane da niyar dawo masu da shi ana gobe zabe sannan a cika masu sauran kudinsu

- Hakazalika jam' iyyar ta yi zargin cewa Ganduje da jam' iyyarsa ta APC na shirin amfani da yan daba wajen magudin zaben

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kano, ta yi zargin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na shirin amfani da siyan kuri’u, hada kai da jami’an tsaro da kuma yan daba wajen yin magudi da tarwatsa zaben da za a sake gudanarwa a jihar.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa jami’an gwamnati na nan suna yaudarar mata ta hanyar basu N5,000 domin su sallama masu katunan zabensu gabannin zaben.

A wata budadiyar wasika ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jiya Laraba, 20 ga watan Maris, jam’iyyar PDP ta bukace da ya yi kira ga dukkanin shugabannin siyasa, malaman addini, yan kasuwa da kuma sarakunan gargajiya a fadin jihar da su nusar da yan siyasa da su rungumi zaman lafiya don ganin ba a samu matsala ba a jihar.

Zaben raba gardama: PDP ta bankado abinda Ganduje da APC ke kulla wa
Zaben raba gardama: PDP ta bankado abinda Ganduje da APC ke kulla wa
Asali: UGC

A wasikar dauke da sa hannun mukaddashin Shugaban PDP na jihar, Rabiu Suleiman Bichi, jam’iyyar tayi zargin cewa gwamnatin jihar ta karbi katunan zabe zuwa gidan gwamnati da niyar dawo da shi ga masu zaben ana gobe zabe sannan ta cika masu N5,000 na kuri’un da ta siya.

Ya ci gaba da zargin cewa tuni an kama wasu da ke gudanar da wannan aiki na zambar wadanda jami’an gwamnati ne kuma an mika su ga yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Shugaban CCT yayi barazanar rufe yan jarida

A cewarsa, a daidai lokacin da ake gudanar da bincike akan masu laifin, musamman wadanda aka kama sannan aka mika su ga jarumin kwamishinan yan sandan jihar, tuni jami’an yan sandan wasu bangare suka saki wasu daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel