‘Yan Majalisan APC na Arewa sun yi ca a kan mukamin Bukola Saraki

‘Yan Majalisan APC na Arewa sun yi ca a kan mukamin Bukola Saraki

Manyan ‘Yan siyasa da kuma ‘Yan majalisun da su ka fito daga yankin Arewa maso gabas da kuma Arewa ta tsakiya sun matsa lamba cewa su za su fito da shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ‘Yan majalisan yankunan Arewa ta tsakiya da gabas sun tasa jam’iyyar APC mai mulki a gaba domin a ba su damar tsaida wanda zai jagoranci ragamar majalisar dattawan kasar a majalisa ta 9.

Manyan Sanatoci da tsofaffin gwamnoni su na kokarin ganin an karkato da mukaman majalisar yadda na-kusa da su za su samu. Da alamu APC za ta bayyana yankunan da za su rike mukaman majalisa da zarar an gama zaben gwamnoni.

KU KARANTA: Ba za ayi zaben cike-gibi na gwamna a Adamawa ba inji babban kotu

‘Yan Majalisan APC na Arewa sun yi ca a kan mukamin Bukola Saraki
Jigon APC Tinubu yana so Matar sa ta zama Mataimakiyar Shugaban Majalisa
Asali: UGC

Rashin tsara yankunan da za su rike mukamai na iya sake kawowa gwamnatin APC cikas a majalisa kamar yadda aka yi a baya. Shi dai Jigon APC Bola Tinubu yana kokarin ganin Mai dakin sa ta zama mataimakiyar shugaban majalisa.

Wasu Sanatocin kasar su na ganin ya kamata a ba Yankin Arewa ta Gabas dama su fito da shugaban majalisa a wannan karo. Arewa ta tsakiya ce ta kawo shugabanni irin su Iorchia Ayu, Ameh Ebute, David Mark da kuma Bukola Saraki.

Daga yankin Arewa ta gabas din ana fitita Sanata Ahmad Lawan da kuma Mohammed Danjuma Goje da kuma Mohammed Ali Ndume wanda kowanen su ya dade a majalisar. Sai kuma Abdullahi Adamu da ya fito daga yankin Arewa ta tsakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel