Shugaban CCT yayi barazanar rufe yan jarida

Shugaban CCT yayi barazanar rufe yan jarida

Danladi Umar, Shugaban kotun kula da da’ar ma’aikata (CCT), yace ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tura kowani dan jarida da ke murguda gaskiya gidan yari ba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Umar ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris a lokacin da yake martani ga kanun labaran jaridu a zaben karshe da aka yi.

Alkalin na CCT yayi zargin cewa wasu jaridu sun murguda gaskiya a lokacin da suka kawo rahoyon cewa Walter Onnoghen, dakataccen Shugaban alkalan Najeriya, ya zargi gwamnatin tarayya da sauya takardar da ya kaddamar da kadarorinsa.

Onnoghen dai na fuskantar tuhume-tuhume shida akan kaddamar da kadarorin karya.

Shugaban CCT yayi barazanar rufe yan jarida
Shugaban CCT yayi barazanar rufe yan jarida
Asali: UGC

Umar yace Adeboyega Awomolo, lauyan gwamnatin tarayya, ya dai kawai bayyana takardar da aka gabatar a zaman karshe a maatsayin kwantancce.

“Akwai yan jarida anan?” Umar ya tambaya.

Ya kara da cewa: “Akwai rahotanni da aka wallafa, guda uku. Bari na fara da daya. Shafin farko na jarida ta ruwaito cewa: ‘Onnoghen ya zargi gwamnatin tarayya da sauya takardar kaddamar da kadarorinsa’. A kula sauyi.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na shiga harkar siyasa gadan-gadan – Ali Nuhu

“Wani kuma: ‘Onnoghen ya zargi gwamnatin tarayya da wasa da takardar kaddamar da kadarorinsa.”Duk wadannan makirci ne, da kuma murguda gaskiyar abunda ya wakana.

“Kun yi sa’a sosai a yau, da nayi amfani da cikakken ikon wannan kotu sannan na tura ku gidan yari. Ba zan yi kasa a gwiwa ba waje yin maganin duk wani dan jarida ya sauya gaskiya.

“Za ku tsaya a can har zuwa lokacin da zan yi ritaya wato shekaru 28 masu zuwa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel