Dalilin da ya sa na shiga harkar siyasa gadan-gadan – Ali Nuhu

Dalilin da ya sa na shiga harkar siyasa gadan-gadan – Ali Nuhu

- Jarumin wasan Hausa, Ali Nuhu ya bayyana dalilinsa na tsunduma a harkar siyasa

- Ali yace an saba ganin yan fim a harkoki na siyasa shiyasa a wannan karon shima ya shiga domin a dama da shi

- Sarkin Kannywood kamar yadda ake masa lakabi yace banbancin ra'ayi na siyasa da ya shiga tsakaninsa da wasu abokan sana'arsa bai kawo rashin jituwa ba ko kadan a wajen mu'amalarsu

Fitaccen jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan Hausa wanda ake yi wa lakabi da sarkin Kannwood, Ali Nuhu ya bayyana cewa ba sabon abu ne ganin yan fim su fada harkokin siyasa, kamar yadda 'yan wasan Hausa tsunduma ciki a yanzu.

Ali ya ce an saba ganin 'yan wasa na shiga harkar siyasa a duniya "kuma su zabi bangaren da suke muradi. Wannan shi ne dalili na farko da ya sa na ji cewa ni ma wannan karon ya kamata a dama da ni,".

Dalilin da ya sa na shiga harkar siyasa gadan-gadan – Ali Nuhu
Dalilin da ya sa na shiga harkar siyasa gadan-gadan – Ali Nuhu
Asali: Depositphotos

Jarumin ya kuma bayar da tabbbacin cewa daukar bangaren da suke yi a siyasa, ba zai jawo cikas ga sana'arsu ba.

Har ila yau, ya ce bambancin siyasar da ke tsakaninsu da abokan sana'arsa bai jawo wni rigima ko rashin jituwa ba a tsakaninsu.

KU KARANTA KUMA: Rundunan yan sandan Edo ta ceto basaraken da masu garkuwa da mutane suka sace

Daga karshe Ali ya ce ba ya tunanin wasu masoyansa za su iya juya masa baya saboda suna goyon bangaren siyasa daban da nasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel